'Yan Gudunhijira Miliyan 60 Na Bukatar Taimako Inji Ban Ki-moon

  • Ibrahim Garba

Wasu 'yan gudunhijira

Yayin da tashe-tashen hankula a sassan duniya ke kara yawan 'yan gudun hijira, an yi kiran da a tallafa masu, ganin yadda wahalarsu ke karuwa.

Sakatare-Janar din MDD Ban Ki-moon ya yi amfani da Ranar 'Yan Gudun Hijira ta Duniya, wadda jiya ce, wajen kiran da a tuna da wahakar mutane kusan miliyan 60, wadanda tashe-tashen hankula da kuntatawa su ka sa su barin muhallansu bara.

A wata takardar jawabi jiya Asabar, Mr Ban ya bukaci al'ummar duniya da ta "mutunta rayuwar dan'adam, yayin da ta ke jaddada zaman hakuri da juna."

Ya alakanta karuwar 'yan gudun hijira fiye da abin da aka taba gani da tashe-tahen hankulan Syria da Iraki da Ukraine da Sudan Ta Kudu da Janhuriyar Afirka Ta Tsakiya da Najeriya da kuma sassan Pakistan.

Ya ce wannan na nuna cewa, "a yanzu daga cikin mutane 122, mutum guda dan gudun hijira ne ko wanda ya rasa muhallinsa ne ko kuma mai nemar mafaka ne. Alkaluman MDD na nuna cewa kimanin mutane 42,500 su ka zama 'yan gudun hijira kullu yaumin a shekara ta 2014 -- wato a cikin shekara 4, ya ribanya na baya har sau hudu.