To amma yanzu da alama Uganda din ta soma jin jiki daga wannan nauyin, ta soma neman agajin kasashen duniya.
Frayim-Ministan Uganda, Ruhakana Rugunda, yace a cikin watani shidda da suka gabata, kusan kullum sai Uganda ta karbi bakunci mutane kamar 2,000 dake gudun hijira, abinda yace yana dada nauyi akan hukumomin kasar a kokarinsu na samarda kayan masarufi kamar ruwan sha, kiyon lafiya da ilimi.
Dangane da hakan ne aka shirya cewa a watan gobe, shugaban Uganda din, Yoweri Museveni, da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ko MDD, Antonio Guterres da kuma shugabannin hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD din zasu jagoranci wani taron bude asusun neman tallafin Dala milyan dubu 2 a kowace shekara, har tsawon shekaru hudu, don gudanar da aikin kula da ‘yan gudun hijiran.