'Yan Gudun Hijira daga Adamawa Sun Samu Mafaka a Kano

Yan gudun hijira.

Biyo bayan hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram suka kaddamar a jihar Adamawa jama'a da dama suka fantsama zuwa wurare daban daban

Wadanda suka samu suka isa Kano sun samu mafaka mai kyau sabili da tanadi da aka yi masu.

Wasu da aka zanta dasu sun ce tunda suka isa Kano basu da wata damuwa. Daga su har iyalansu suna ci suna sha ana kuma basu suturar sawa da kayan kwanciya da kayan wanka da na ado.

Galibin 'yan gudun hijiran mata ne da kananan yara. Banda hukumar bada agajin gaggawa hukumar hisba ma na kan gaba wurin kula da 'yan gudun hijiran. Malama Zara Muhammed Umar kwamandar kula da al'amuran mata da yara ta hukumar hisba tace gwamnati ta turota ta ga menene suke ciki. Nawa ne adadinsu. Yaya kananan yara, yaya manyan? Za'a mikawa gwamnatin bayanan da aka tattara. Gwamnati ta turo tallafin farko a fara yi masu abinci kafin a san abun da za'a yi.

Akwai kuma kungiyoyi da suke ta taimakawa babu rike hannun yaro. To saidai duk da haka ana bukatan kayan abinci musamman na karin kumallo. Akwai bukatar a tallafawa matasan da aikin yi. Kamfanoni da masu hannu da shuni suna iya kirkiro ayyuka su yi sadaka dasu.

Wata kungiya tace banda bada tallafi kungiyar ta maida hankali akan kwantar da hankulan masu gudun hijiran ganin cewa da yawa sun kadu.

Hukumar hisba ta aika da likitoci domin su kula da mutanen domin akwai gajiya da rashin jin dadin jiki. Ga kuma mata masu ciki.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Gudun Hijira daga Adamawa Sun Samu Mafaka a Kano - 3' 44"