'Yan Gudun Hijira 2,500 Su Ka Gudu Daga Najeriya Zuwa Niger A Rana Daya

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da ake kira UNHCR a takaice ta fadi cewa karuwar tashe-tashen hankali, da munanan hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa a arewa maso gabashin Najeriya na sanya dubban ‘yan gudun hijira guduwa zuwa jamhuriyar Niger. Hukumar ta ce yanayin na haifar da wani sabon tashin hankalin taimakon agajin gaggawa a yankin iyakar kasashen biyu.

Hukumar ta UNHCR ta bada rahoton cewa ‘yan Najeriya fiye da 40,000 su ka tsere zuwa Niger a cikin watanni 10 da su ka gabata. Hukumar ta kuma ce kusan rabinsu tun daga karshen watan Mayu suka isa Niger.

A rana daya kacal, ranar 11 ga watan Satunba, hukumar ta ce fararen hula sama da 2,500, da kungiyoyin ‘yan bindiga a Najeriya suka kaiwa hari ne suka yi gudun tsira da rayukansu.

Mai magana da yawun hukumar ta UNHCR, Babar Baloch ya fadawa Muryar Amurka cewa ‘yan bindigar da su ke kai wadannan hare-haren akan fararen hula ba su da alaka da ‘yan boko haram. Tun dai daga shekarar 2009, kungiyar ‘yan boko haram ta kashe mutane fiye da 30,000, miliyoyin jama’a kuma sun rasa matsugunnansu, bayan haka an sami tashin hankalin taimakon agaji mai muni. Baloch ya ce ‘yan gudun hijirar da ke isa Nijer a rikide su ke zuwa.