Wannan na zuwa ne lokacin da bayanai ke nuna fargaba akan yiwuwar ‘yan fashin daji zasu iya karbe ikon gudanar da jagorancin wasu yankuna a kasar.
Bayanan da ke fitowa daga sassa daban daban na arewacin Najeriya na nuni akan cewa har yanzu ‘yan fashin daji na cin karen su babu babbaka a yankunan.
Matakan da mahukumta ke dauka na shawo kan matsalolin rashin tsaron ya zuwa yanzu ba su iya magance matsalolin baki dayan su ba.
Har wasu jama'a na kallon cewa gwamnatin kasar tafi fifita lamarin siyasa bisa ga tsaron rayukan jama'ar yankunan da ke fama da rashin tsaro musamman duba da tanadin tsaro da aka yi a zaben jihar Anambara da aka gudanar karshen makon nan.
Daya daga cikin wakilan jama'ar gabashin Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya Sa'idu Ibrahim Naino yana cikin masu wannan ra'ayin.
Ko a makonnin baya ‘yan fashin daji sun kakabawa wasu al'ummomi haraji duk da yake rundunar ‘yan sandan kasar ta musanta wannan zancen, abinda wasu ke ganin da an samar da isassun jami'an tsaro da hakan bai faru ba.
Wannan yanayin da abubuwan da ke ci gaba da faruwa na haifar da fargaba akan ganin akwai yuwuwar ‘yan fashin daji su iya karbe ikon wasu garuruwa a cewar tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Birni, Idris Muhammad Gobir.
Kawo zuwa hada wannan rahoton Muryar Amurka bata samu jin ko ga bincika ba, ko abin gaskiya ne, ko akasin haka.
Matsalolin rashin tsaro dai a iya cewa sun gagari magani a arewacin Najeriya duk da yaki mahukumta na iya kokarin su na shawo kansu.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5