To sai dai rundunar ‘yan sandan kasar ta ce babu tabbas ga wannan batun kuma tana daukar matakai ko da zancen ya zamo gaskiya.
Tabarbarewar lamarin tsaro a Najeriya musamman a yankin arewa yana ci gaba da daukar sabon salo a kokarin da ‘yan fashin daji ke yi na kara wanzar da ayukkan su a yankunan kasar.
Rahotanni sun nuna cewa bayan kakabawa mutane haraji da ‘yan bindiga ke yi, yanzu suna nada hakimai ga jama'ar da suka saura basu yi hijira ba a wasu yankunan gabashin Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya.
Wani mazaunin yankin Idris Muhammad Gobir ya ce ya zuwa yanzu ‘yan fashin daji sun nada hakimai biyu a yankin na Sabon birni.
Wani mazaunin yankin na gabashin Sakkwato Bashir Altine Guyawa yace tun kafin ‘yan bindigar su ayyana nadin hakimai sun da dadewa suke da iko da wasu yankunan yankin.
To ko mi hakan yake nufi ga kasa irin Najeriya a samu ‘yan bindiga su karbe iko da wasu yankuna?
Detective Awal Bala Durumin iya yace akwai hadarin gaske ga lamarin.
A nata haujin rundunar ‘yan sandan kasar ta fitar da wani bayani mai dauke da sa hannun kakakinta a Sakkwato ASP Sanusi Abubakar inda ta bayyana cewa bincike ya tabbatar da labarin a zaman maras tabbas kuma tace tana kan daukar kwararan matakai na gano inda wadannan korafe korafe suka samo asali.
Tace tuni akwai aikin fatattakar yan bindiga ake yi karkashin shirin hadarin daji wanda ya kunshi sojojin sama dana kasa da yan sanda kuma bada jimawa ba za'a kai farmaki a sansaninin ‘yan fashin daji domin maido da zaman lafiya a yankunan da rashin tsaro ya daidaita.
Yanzu jama'a dai sun zura ido su ga yadda zata kaya da yake wannan talatar ce za'a bude kasuwa a gangara karkashin jagorancin dan Bindiga Hassan.
Saurari cikakken rahaton a cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5