Hanyar nada tsawon kilomita dari biyu da talatin ne kawai daga biranen biyu.
Idan hanyar nada kyau tafiyar awa biyu ne kawai amma yanzu sai mutum ya kwashe awa goma sha hudu yana fafatawa a hanyar saboda mugun yanayin da take ciki.
Hanyar nada mahimmanci wajen zirga zirgan kasuwanci tsakanin kasashen biyu. To saidai 'yan ta'adan Boko Haram suna tare masu balaguro akan hanyar suna yi masu fashi da makami. Suna kwace masu kudade da kayan abinci kana su tsere su shiga dajin Sambisa.
Direbobin da aka zanta dasu sun ce suna wahala matuka. Baicin hasarar dukiyoyinsu 'yan ta'adan na kashe 'yanuwansu ko kuma a yi garkuwa dasu cikin daji.
Gwamnatin Kamaru ta ba wani kamfanin kasar China kwangilar sake gina hanyar amma 'yan Boko Haram suka yi awon gaba da ma'aikatan kuma har yanzu shiru a keji, babu duriyar 'yan Chinan da aka sace.
Ga rahoton Awal Garba da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5