Kawo yanzu dai ba'a san adadin mutanen da kungiyar ta kashe ba.
Babu abun da 'yan kungiyar Boko Haram suka bari kama daga mutane zuwa gidaje da dabbobi, kai har ma da itatuwa.
Mr Adamu Kamale mai wakiltar yankin a majalisar dokokin jihar Adamawa ya bukaci a kai masu doki. Ya lissafa kauyukan da aka kone kuma ya kara da cewa fiye da kashi hamsin na al'ummar yankin sun yi asarar rayukansu. Ya kira gwamnati ta tura dakarunta domin kwato yankin daga hannun 'yan Boko Haram da kuma kawo karshen kashe-kashe da ake yi.
Har yanzu jami'an tsaro basu ce uffan ba akan hare-haren da aka cigaba da kaiwa yankin. To saidai kungiyar maharba da 'yan kato da gora sun ce suna kokarin kwato yankin. Sun bukaci gwamnatocin Borno da Yobe su fito su bada tasu gudunmawar.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5