'Yan Boko Haram Sun Kai Hari Kasar Kamaru

Boko Haram

'Yan Boko Haram sun cafke mutane fiye da hamsin a kasar Kamaru tare da kone gidaje tamanin

A kamaru jami'an kasar sun bada labarin cewa mayakan Boko Haram sun kama akalla mutane sittin a wani harin da suka kai bayan da suka tsallako daga Najeriya.

Jami'an suka ce an kashe mutane masu yawa wadanda suka yi kokarin tare maharan, suka kuma kona gidaje kimanin 80 kurmus.

Ministan yada labaran kasar Issa Tchiroma Bakary, ya kira maharan da cewa basu da imani da rashin mutunta dokoki, kuma ran mutum ba akan kome yake ba a gunsu.

Sace mutanen wadand suka hada da yara, yazo ne kwana daya bayan da kasar Chadi ta tura dubban sojojinta zuwa Kamaru domin su taimakawa kasar ta yaki Boko Haram-kungiyar mayakan da take ikirarin musulunci, da shugabannin Afirka suka ce cikin hanzari tana zama barzana ga yankin baki daya.

Kungiyar tana ta kama kasa akan iyakokin Najerya da Chadi. A baya bayan nan kungiyar ta kama Baga dake kusa da tafkin Chadi, da hallaka mazauna yankin masu yawa.