Karamar Hukumar Mafa ta jahar Borno ta fuskanci hare-haren Boko Haram, wadanda su ka yi sanadin mutuwar mutane 6 a wasu kauyuka, al’amarin da ya sa mutanen wadannan kauyukan gudu zuwa Maiduguri, hedikwatar jahar tun daga shekaran jiya.
‘Yan gudun hijirar da su ka isa Maidugurin sun kai sama da 600, ciki da mata da yara da kuma dabbobinsu irin shanu da tumaki da jakuna da sauransu. Gwamnatin jahar ta tura tawagar tarbar ‘yan gudun hijirtar karkashin Shugaban Hukumar Samar Da Agajin Gaggawa injiniya Ahmed Satomi, wanda ya ce yanzu ‘yan Boko Haram sun zama barayi kawai.
Shugaban Karamar Hukumar Mafan, Honorabul Shattima Lawal Maina ya ce sojoji na cikin Mafa su na samar da tsaro. Ya ce saidai akwai ‘yan Boko Haram jifa-jifa a daji. Y ace saboda ‘yan gudun hijirar na tafe da dabbobinsu babu yadda za a kai su sansanin ‘yan gudun hijira, saidai kawai a samar masu tantuna.
‘Yan gudun hijirar sun bayyana irin wahalhalun da su ka fuskanta lokacin da ‘yan Boko Haram din su ka far ma su.
Ga wakilinmu Haruna Dauda da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5