'Yan Boko Haram Da Suka Tuba Sun Isa Sansanin Koyas Da Sake Hali Dake Gombe

'Yan Boko Haram da suka tuba suna samun koyaswa a sansanin dake Gobe

'Yan Boko Haram 52 da suka tuba suna sansanin koyas da sake hali dake Gombe inda ko a watan jiya ma an yaye wasu guda shida da suka tuba kafin wadannan na yanzu

A cewar kwamandan sansanin, Manjo Janar Shafa yayinda yake ganawa da manema labarai, kawo horas da 'yan Boko Haram da suka tuba shi ne irinsa na biyu saboda a farkon wannan shekarar an horas da wasu guda shida da aka yaye watan jiya.

Kashi na biyu da aka kawo sansanin su ne guda 52 da suka tuba aka kuma tantancesu domin tabbatar da sahihiyar gaskiyar tubansu.

Yayinda suke sansanin zasu yi kwasakwasai da dama da suka hada da gyara halayya da sauya tunane da zamantakewar hulda da jama'a da batun ta'ammali da miyagun kwayoyi.

Akan irin sana'o'in da zasu so su koya domin samun dogaro ga kai, Manjo Janar Shafa yace sun kulla yarjejeniya da hukumar koyas da sana'o'i ta kasa saboda sun bayyana irin sana'o'in da suke so su yi. Akwai masu sha'awar dinki,walda, noma,kafinta, da aikin makanikanci.

Bayan sun kammala samun horo Kwamandan yace za'a basu kayan da zasu yi sana'o'insu tare da karamin bashin kudi da zai zama masu jari bayan sun koma cikin al'ummominsu.

Sale Muhammad da yayi magana a madadin yan Boko Haram din yace sun godewa Allah da aka karbesu da hannu biyu kuma zasu yi iyakacin kokarinsu domin kada su ba gwamnati kunya.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Boko Haram da Suka Tuba Sun Isa Sansanin Koyas da Sake Hali dake Gombe - 3' 23"