'Yan Bindigar Yankin Niger Delta Sun Ce Za Su Koma Kai Hare-Hare

An kwashe dan lokaci mai tsawo da samun lafawar rigingimun ‘yan bindigar yankin Niger Delta dake kai hare-hare a harabobin ayyukan mai, sai dai kuma barazanar kai wadannan hare-haren na neman dawowa.

Yanzu kungiyoyin ‘yan bindiga dabam dabam na yankin Niger Delta sun fito da sanarwar cewar sun gaji da “gafara sa ba suga kaho ba,” ta fuskar gwamnatin tarayyar Najeriya, sun kuma ce za su koma cikin lungunan ruwayen yankin na Niger Delta domin su dauki makamai tare da cigaba da kai hare-hare a wuraren ayyukan mai, musamman farfasa bututun mai.

Kungiyar Niger Delta mai suna Avengers, wadda ita ce ta fi kai munanan hare-hare, ita ce ta fara bada sanarwar cewar hakurinta a kai bango, ta kuma yi barazanar komawa kai hare-hare a yankin mai arzikin man fetur. Bayan kungiyar Avengers, wasu kungiyoyin 'yan bindiga suma sun yi barazanar fara kai hare-hare.

A wata tattauanwa da sasahen hausa, mai Magana da yawun rundunar gamayyar jami’an tsaro ta musamman da ake kira Operation Delta Safe, Manjo Ibrahim Abdullahi, wanda yace ba za su yi kasa a guywa ba, duk wata barazana daga wata kungiyar tsagera ba zata hana su aikinsu ba.

Kwanana nan dattawan yankin Niger Delta da yankin ya dorawa alhakin tattaunawa da gwamnatin tarayyar Najeriya sun yi wani zama inda suka tattauna akan matsalolin dake addabar yankin, inda suka zargi gwamnatin Najeriya akan cewa tura dakarun tsaron da ta yi yankin na kara dagula al’amura da kuma tunzura ‘yan bindigar yankin.

Mai Magana da yawun gwamnatin Najeriya Malam Garba Shehu, y ace wannan tamkar zagon kasa ne akewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, saboda ai sai an hako man sannan jihohin dake yanken za su iya samun kason da ake basu.

Za ku ji Karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan bindigar yankin Niger Delta sunce za su koma kai hare hare - 3'28"