Tashe-tshen hankulan da 'yanbindigan suka yi can baya ya yi tasiri akan tattalin arzikin kasar Najeriya saboda fasa bututun mai tare da hana hakoshi a wasu wuraren.
Ziyarar da wata tawagar 'yan jarida da ta hada da wakilin Muryar Amurka ta kai a wani yankin Niger Delta ya nuna irin yadda matasan yankin suka soma fasa bututun mai. Matasa zauna gari banza da 'yan bindigan su ne suke yawan fasa bututun mai yanzu tare da tada hankulan mutane..
Yayin ziyarar sun tarar da wasu gungun matasa suna kokarin balle kofar shiga kamfanin Shell mai hako danyan mai a yankin a garin Nembe.
Can baya sulhun da aka yi dasu tare da sasu cikin harkokin gwamnati ya sa an samu kwanciyar hankali kafin yanzu su soma kokarin komawa tada hankali. Alal misali sace turawa ya ragu, sace mai ma ya ragu amma basu daina ba.
Marigayi shugaba 'Yar'Adua shi ya yi wa 'yan bindigan ahuwa tare da horas da dubu talatin cikinsu bisa sana'o'i daban daban. Su ne kuma aka dauka aikin tsare bututun mai. Wannan shirin shugaba Goodluck Jonathan ya cigaba dashi. Sai dai abun takaici shi ne da yawa cikinsu suna gararamba saboda babu abun yi kuma suna cike da korafe korafe.
Wata Madam Peter Nangbe tace matansu suna mutuwa saboda yunwa, 'ya'yansu basa makaranta, su kansu basu da cikakken koshin lafiya kuma sai wahala suke sha.
Tunda shugaba Jonathan ya fadi zaben 2015 'yan bindigan yankin suka yi barazanar sake daukan makamai su soma fasa bututun mai tare da tada hankalin jama'a. Kamar yadda suka sha alwashin yi sun soma fasa bututun mai a wasu wurare.
Barazanar ta 'yan bindigan ka iya mayar da kasar gidan jiya.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5