Shugaban Najeriya yayi taron tattaunawan ne da nufin shawo kan riginrimun da mayakan suka jefa yankin Niger Delta ciki har ma sun shafi hakar man fetur.
To saidai maimakon hare-haren su ragu bayan ganawar da dattawansu sai gashi kwatsam karuwa ma su keyi. Kamfanonin mai da yawa ne yanzu mayakan suka kai ma hari tare da yi masu barna matuka.
An samu rarrabuwar kawuna da kungiyoyin dake tada kayar bayan inda kowannensu ya sha gaban kansa ba tare da yin la'akari da komi ba. Kowace kabila nada nata muradun haka ma dattawan yankin da yanzu an gani a fili cewa basu da wata martaba a idanun mayakan.
Da wuya a samu wata masalaha idan ba'a samu wakilai daga kowane bangare ba. Harin baya bayan nan da tsagerun suka kai ya dada firgita jama'a saboda ya kawo cikas a harkokin hakko danyan mai a yankin. Mayakan sun fasa bututun mai masu mahimmanci dake aika danyen mai zuwa kasashen waje na kamfanoni guda uku.
Wani dattijon yankin yace suna cikin wata irin rayuwa ce inda babu wanda yake ganin girman kowa saboda haka ana tababan irin mutunci da dattawan ke dashi a idanun mayakan.
Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5