'Yan Bindiga Sun Yi Kisan Kiyashi a Kaduna

Wani yanki da aka kai hari a arewacin Najeriya

Wasu 'yan bindiga sun kone garin Marina sannan suka shiga garin Kerawa da ke Karamar hukumar Igabi inda suka hallaka mutane da dama sannan suka kone motoci da dama.

Al'umar yankin da 'yan bindigan suka afkawa sun ce da safiyar Lahadi maharan suka yi wa garin kawanya inda suka kwashe sa'o'i suna harbin kan mai-uwa-da-wabi.

Daya daga cikin shugabannin 'yan-sintiri a yankin wanda ya sakaya sunansa ya ce maharan sun kwashe sa'o'i uku zuwa hudu suna cin karensu ba babbaka.

A baya dai yankin Kerawa da ke karamar hukumar ta Igabi na kokawa ne da masu garkuwa da mutane amma a wannan karon kansilan yanki Alh. Dayyabu kerawa ya ce abin ya sha banban.

Har ya zuwa daren jiya Lahadin gwamnatin jihar Kaduna ba ta ce komai ba tukuna yayin da rundunar 'yan sandan jihar ta ce tana tattara bayanai tukuna.

Ko da yake, wasu al'umar yankin sun ce jami'an tsaro sun kai dauki yankin da aka kai harin daga baya.

Saurari cikakken rahoton Isa Lawal Ikara daga Kaduna:

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Bindiga Sun Yi Kisan Kiyashi a Kaduna - 3'53"