'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Magajin Garin Daura

Shugaba Buhari A Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa Na Sake Neman Wa'adin Shugabanci

Yan bindiga sun dauke magajin garin Daura jim kadan bayan idar da sallar magariba

‘Yan bindigar dan sun shiga cikin garin Daura suna harbe-harbe inda su ka yi awon gaba da magajin garin Alhaji Musa Umar.

Magajin Garin wanda shi ne hakimin garin na Daura mai tarihi a jihar Katsina, ya gamu da akasin ne bayan ya dawo daga masallaci ya zauna da wasu jama’a a kofar gidan sa.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, maharan sun isa gidansa ne da mota kirar FIJO 406 suka yi ta harbi don firgita jama’a kafin dauke magajin gari. Lamarin ya zama da tada hankali da ya kasancewa gidanshi yana tsakiyar babban garin Daura, aka kuma dauke hakimin gari ba tare da samun turjiya ba.

In za a tuna Hakimin Malumfashi ma marigayi Jostis Mamman Nasir ya taba cin karo da masu satar mtanen amma Allah ya kubutar da shi.

Yankin Kaduna,Katsina da Zamfara sun zama cikin halin damuwa ta masu satar mutane don samun kudin fansa da wani lokacin ya kan kai ga rasa rayuka.

Saurari hirar Nasiru Adamu El-hikaya da Alh Ya'u Chiroman Bakan Daura

Your browser doesn’t support HTML5

An sace magajin garin Daura-3:30"