Al’ummomin garin Udawa da kewaye da ke karamar hukumar Chukun a jihar Kaduna a Najeriya sun ce hare-haren 'yan bindiga na hana su noma kuma na kuma neman hana karatun boko. sun kuma ce daruruwan 'yan bindiga da ke yawan kai hari a garuruwan yankin sun sanya akasarin mazauna yankin gudun hijira.
WASHINGTON, D.C. —
Al’ummomin garuruwan da ke yankin Udawan, karamar hukumar Chukun sun ce banda dalibai shida da ke rubuta jarabawar WEAC da aka sace, akwai wasu mutane ma da su ka kashe watanni ba a sako su ba.
Hare-haren 'yan bindiga a wasu yankunanan jihar Kaduna dai sun hana al'umma da dama sukuni amma gwamnatin jihar Kaduna ta ce tana dukkan mai yuwuwa don kawo karshen wadannan hare-hare, Inji Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida malam Samuel Aruwan.
Hare-haren 'yan bindiga a yankunan karkara dai sun hana manoma da dama zuwa gona wanda wasu ke fargabar hakan zai iya haifar da karancin abinci a Najeriya.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara.
Your browser doesn’t support HTML5