'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Sanda 8 a Jihar Kogi


Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton barayin banki ne sun yi dirar mikiya a garin Isanlu da ke yankin karamar hukumar Yagba ta Gabas a jihar Kogi ranar 4 ga watan Juni inda suka kashe mutum 9.

'Yan bindigar sun afka bankin ajiyar First Bank da ke yankin ne bayan da suka hallaka 'yan sanda 8 ciki har da wani DPO, suka kwashe makaman 'yan sandan suka kuma kashe wata mata da ta je kai ajiya bankin, a cewar wani mazaunin yanki da ya nemi a sakaya sunansa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da aukuwar wannan al’amarin. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ASP William Aya, ya ce tuni aka tura karin jami’an tsaro a yankin. Ya kuma ce babu wanda aka kama a lokacin amma an riga an fara gudanar da bincike.

William ya ce a hukumace dai mutum 8 ne suka tabbatar da mutuwarsu kuma jami'an 'yan sanda ne.

A wata sanarwa da gwamnatin jihar Kogi ta fitar ta jajantawa iyalan wadanda lamarin ya shafa, gwamnan jihar Alhaji Yahaya Bello ya bukaci jami'an tsaro su tabbata sun gano wadanda suka tafka wannan ta'asa.

Saurara karin bayani a cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Sanda 8 A Jihar Kogi