'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 37 a Jihar Filato

Taron shugabannin addinai kan zaman lafiya a jihar Plateau, Nigeria

Wani kakakin rundunar soja yace 'yan bindiga sun kai hare-hare kan kauyuka 4 yau talata da asuba a Jihar ta Filato
Rundunar sojojin Najeriya ta ce 'yan bindiga sun kashe mutane 37 a tashin hankali na baya-bayan nan a yankin arewa ta tsakiyar kasar.

Wani kakakin rundunar sojoji, Kyaftin Salisu Mustapha, yace 'yan bindigar sun kai hare-hare kan wasu kauyuka guda 4 da asubahin yau talata.

Kakakin yace 'yan bindigar sun tsere a lokacin da sojoji suka isa wurin. Yace sojojin zasu dauki dukkan matakan da zasu iya domin kamo wadanda suka kai wannan farmakin.

Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai wannan harin.

Jihar Filato tana daya daga cikin jihohin da suka raba tsakanin yankin arewacin kasar inda Musulmi suka fi yawa, da kuma yankin kudu inda Kirista suka fi yawa.

An sha samun tashe-tashen hankulan addini da kabilanci a wannan yanki, koda yake kwararru sun ce akasarin wannan tashin hankalin yana samo asali ne daga rikice-rikicen siyasa da na mallakin albarkatu.

Zainab Babaji ta aiko da karin bayani a kan lamarin...

Your browser doesn’t support HTML5

An Kai Farmaki a Jihar Filato - 2:29