Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe Magajin Garin Mamfe da ke jihar Kudu maso yammacin kasar Kamaru.
A ranar Lahadi 10 ga watan Mayu ne aka harbe Ashu Priestley Ojong, garin na Mamfe mai tazarar kilomita 500 daga Yaounde babban birnin kasar.
Duk da cewa gwamnatin kasar ta ce ana kan gudanar da bincike game da kisan, wasu na kyautata zaton ‘yan awaren yankin da ke magana da harshen Ingilishi ne suka aikata kisan.
Alhaji Jibril Ibrahim Mai-Yaki, daya daga cikin masu fada a ji a bangaren ‘yan awaren, ya yi Allah wadai da kisan ya kuma ce kwamitin bincike na musamman ne kadai zai iya tabbatar da wadanda suka aikata kisan.
A cewarsa, ‘yan awaren sun amince su ajiye makamansu don yakin da ake yi da annobar cutar coronavirus.
Alhaji Garba Abbakar, na jam’iyyar RDPC mai mulki, ya ce duk kokarin da gwamnati ke yi shi ne na samar da zaman lafiya amma kuma wasu na kokarin ta da fitina.
Saurari karin bayani cikin sauti Awal Garba.
Your browser doesn’t support HTML5