'Yan Bindiga Sun Kashe Kufdawa 7 a Masar

  • Ibrahim Garba

Kirista Kufdawa na zanga-zanga bayan harin

Kufdawan kasar Masar sun sake ganin abin tashin hankali bayan da wasu 'yan bindiga, wadanda kungiyar ISIS ta ce 'ya'yanta ne, su ka kai hari kan wasu motoci dauke da wasu Kufdawa su ka hallaka bakwai daga cikinsu baya ga wasu 18 da su ka raunata.

A kasar Masar,wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wasu motocin bus-bus masu dauke da Kirista Kufdawa a jiya Jumma'a, su ka kashe bakwai daga cikinsu, wanda shi ne na baya-bayan nan a hare-haren da ake yawan kaiwa kan tsirarin mabiya wasu addinai a kasar.

Maharan sun bude wuta kan motocin bus-bus din a yankin tsakiyar lardin Minya bayan da Kiristan su ka je yin baftisma a majami'ar Samuel.

Majami'ar Kufdawan ta fada a wata takardar sanarwa cewa shida daga cikin wadanda aka kashe din 'yan gida daya ne, kuma akwai wasu mutane 18 da aka raunata a harin. Maharan dai sun arce bayan harin.

Kungiyar ISIS ta yi ikirarin kai harin kwantar baunar, bisa ga sanarawar kafar labaranta ta Amaq.