'Yan bindiga sun kai wa mazauna kauyukan kananan hukumomin Sabon Birni da Isa harin kare-dangi duk a gabashin jihar Sokoto wanda ya yi sanadiyyar salwantar rayuka fiye da 70.
Lamarin tsaro a yankin gabashin Sokoto na ci gaba da ta'azzara inda baya ga wadannan hare-haren da yan ta’adda ke kai wa jama'ar yankin, a Larabar wannan mako sun kai hare-haren kare-dangi a kauyukan sabon birni da isa inda suka yi wa jama’a kisan kiyashi.
Bayanan da muka samu daga wasu mazauna yankunan sun nuna cewa mutanen da aka kashe sun wuce 70.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, tare da rakiyar mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar da shugabannin hukumomin tsaro, sun kai ziyarar gaggawa a yankin na sabon birni domin jajantawa jama’ar akan wannan ibtila'in da ya faru
Gwamnan ya sheda wa jama’ar cewa ya zanta da fadar shugaban kasa kuma an amince zai gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari akan sha'anin tsaro a yankin na gabashin jihar.
Tambuwal ya kuma umurci hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Sokoto da ta yi kiyasin hasarar da aka yi domin bayar da agaji ga jama'ar
Ga karin bayani a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5