‘Yan Bindiga Sun Hallaka Shugaban Jam’iyyar APC A Kebbi

Bako Bala

An garzaya da Bala zuwa cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya dake Birnin Kebbi a jiya Laraba, sai dai an yi rashin sa’a ya mutu sakamakon raunukan harsashin da ya ji.

‘Yan bindiga sun sace tare da hallaka shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Suru ta jihar Kebbi, Bako Bala.

Mashawarci na musamman ga gwamnan Kebbi a kan kafafen talabijin da rediyo, Zaidu Bala, yace ‘yan bindigar sun sace Bala ne a kauyensa tare da harbe shi sannan suka bar gawarsa kwance cikin jini.

An garzaya da Bala zuwa cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya dake Birnin Kebbi a jiya Laraba, sai dai an yi rashin sa’a ya mutu sakamakon raunukan harsashin da ya ji.

Jihar Kebbi na daga cikin jihohin Najeriya dake fama da matsalar ‘yan bindiga.