Mayakan Taliban sun kashe mutane wajen 20 a wasu hare-haren bindigogi da kunar bakin wake a Afghanistan a jiya Asabar, al'amrin da ke jaddada fargabar da ke akwai, 'yan makwanni kawai kafin akasarin dakarun kasa da kasa su fice daga kasar.
A kudancin Afghanistan, 'yan bindigar sun bindige 12 daga cikin masu aikin kau da nakiyoyin da ke binne a lardin Helmand, wanda ya janyo musar wuta da 'yan sanda.
Kafar labarai ta Reuters ta ruwaito cewa an hallaka hudu daga cikin maharan a wannan musayar wutar sannan an damke uku.
Tun kafin nan a jiya Asabar din, 'yan sandan Afghanistan sun ce wasu 'yan bindiga sun harbe wani babban jami'in kotun kolin Afghanistan, mai suna Atiqullah Rawoofi, daura da gidansa da ke bayan garin Kabul, babban birnin kasar. Taliban ta ce ita ta kashe Rawoofi amma ba ta fadi dalili ba.
A birnin Kabul kuma, wata fashewa ta bararraka wata motar bus mai dauke da sojojin Afghanistan, ta hallaka akalla mutane shida ta kuma raunata sama da goma.
A wani al'amarin kuma na daban, sojojin taron dangin kasa da kasa sun fadi a jiya Asabar din cewa, wani harin da Taliban ta kai daura da dan filin jirgin saman dakarun Amurka da ke Bagram arewa da Kabul a ranar Jumma'a, ya hallaka sojojin NATO biyu.