'Yan Bindiga Sanye da Kaki Na Adawa Da Shugaban Kasar Kamaru

Shugaba Paul Biya mai mulkin kasar Kamaru tun shekarar 1982.

'Yan bindigar masu adawa sun bude wuta kan wata babbar gada a Douala.

Jami’an gwamnati da kuma shaidun gani da ido a kasar Kamaru sun ce ‘yan bindiga sanye da kayan sojoji kuma dauke da kwalaye na nuna adawa da shugaban kasar da ya jima kan karagar mulki, sun bude wuta kan wata muhimmiyar gada a Douala, cibiyar harkokin kasuwanci ta Kamaru. Shaidu sun ce ‘yan bindigar sun tare gadar Wouri wadda aka cika yawan bi, suka shafe sa’o’i da dama su na musayar wuta da jami’an tsaro a safiyar yau alhamis.

Ba a san yawan wadannan ‘yan bindigar ba. Akwai rahotannin da ke cewa jami’an tsaro sun kama mutane hudu, kuma daya daga cikin ‘yan bindigar ya fada cikin kogin da wannan gada ta bi ta kai.

Jami’an tsaro sun ce wadannan ‘yan bindiga su na dauke da kwalayen da ke bayyana shugaba Paul Biya a matsayin mai mulkin kama-karya, su na kuma fadin cewa tilas ne ya bar mulki ko ta halin kaka.

Kasar Kamaru tana shirin gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 9 ga wata mai zuwa na Oktoba. Shugaba Paul Biya shi yake mulkin kasar Kamaru tun shekarar 1982, watau shekaru 29 da suka shige, kuma ana kyautata zaton zai sake lashe wani sabon wa’adi na shekaru 7.

A shekarar 2008, Mr. Biya mai shekaru 78 da haihuwa, ya sauya tsarin mulkin kasar ya kawar da yawan wa’adin da aka kayyade ma shugaba kan karagar mulki. Sauya tsarin mulkin ya haddasa yamutsin nuna kin-jinin gwamnati inda har aka kashe mutane akalla 40.