Yan Bidiga Sun Kashe Mutane 16 A Masallacin Garin Maza-Kuka

Jana'izar wadansu mutane da 'yan bindiga suka kashe a Zamfara

Wasu 'yan bindiga dauke da manyan makamai sun hallaka mutane fiye da goma sha biyar lokacin da su ke sallar asubahin ranar Litanin a jihar Neja dake Tarayyar Nigeria,

Wannan al'amari dai da ya faru a garin Maza- Kuka da ke yankin karamar hukumar Mashegu ta Arewacin jihar Nejan ya jefa mazauna yankin cikin wani yanayi na tashin hankali,

Wani Tsohon Dan Majalisar Dokokin Jihar da ya fito daga yankin Abdulkareem Maza Kuka yace ko baya ga wadanda aka kashen maharan sun yi awan gaba da wasu masu sallar

ASP Abubakar Dan Inna kakakin rundunar 'yan sandan jihar Neja

Gwamnatin jihar Nejan dai ta tabbatar da kai wannan hari na Masallacin Maza kukan, A hirar shi da Muryar Amurka, sakataren gwamnatin jihar Nejan Alh.Ahmed Ibrahim Matane wanda shima dan asalin wannan yanki ne ya ce bayanan da su ka samu daga mutanen yankin na nuni da cewa, mutane 16 ne aka kashe a masallacin.

A fannin jami'an tsaro kuma, rundunar 'yan sandan jihar Nejan ta tabbatar da kai wannan hari ta bakin kwamishinan 'yan sandan jihar Monday Bala Kuryas wanda ya bayyana cewa, zuwa lokacin da Muryar Amurka ta tuntube shi, basu da adadin mutanen da aka kashe a masallacin dama wadanda aka yi awon gaba dasu, sai dai ya ce sun tura karin jami,an tsaro a wannan yanki mai iyaka da gandun dajin nan na Kayinji,

Mayakan Boko Haram

Tun a cikin makon jiya ne dai 'yan bindigar ke kara zafafa hare haren dake hallaka jama'a a sassa daban daban na jihar Nejan al'amarin da masana ke nuna bukatar ganin gwamnatin jihar ta kara matsa lamba ga gwamnatin Najeriya domin shawo kan Lamarin

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:

Your browser doesn’t support HTML5

Yan bindiga sun kashe mutane a masallacin Maza-Kuka-3:00"