WASHINGTON D.C. —
A ci gaba da neman mafita ga matsalar tsaro a Nijeriya, Majalisar dinkin duniya, karkashin shirin taimakawa kasashe masu tasowa, ta horadda ‘yan kato da gora, ‘yan banga da mafarauta.
Majalisar ta koyar da su dabarun cudanya da al’umma da hada kai da jami’an tsaro, don samun mafita kan matsalar tsaro a Arewa maso gabashin Najeriya.
Matasa dari hudu ne daga jihohin Adamawa da Yobe, suka zo cibiyar koyar da dabarun shugabanci da zama dan kasa na gari a Jos jihar Filato.
An horar da su yadda zasu kaucewa take hakkin dan adam, fahimtar darajar al’adun al’umma da hadin kai wajen gudanar da aikinsu ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba.
Ga cikakken Rahoton cikin sauti daga Zainab Babaji a Jos.
Your browser doesn’t support HTML5