'Yan Aware Sun Kashe 11 a Indiya

​Hukumomin jahar Assam ta arewa maso gabashin kasar Indiya sun ce 'yan awaren wata kabila sun kashe mutane 11.
Sau biyu aka kai hare-hare da yammacin jiya Alhamis a lokacin da mutane ke gidajen su su na bacci.

'Yan sanda sun ce 'yan tawaye mayakan haramtacciyar kungiyar National Democratic Front of Bodoland ne suka bude wuta a gundumar Kokrajhar, suka kashe mutane 8. Kuma suka kashe wasu mutum uku a cikin wani hari na daban da suka kai gundumar Baksa. Aka ce wadanda aka kashen Musulmi ne.

Wannan tashin hankali ya wakana ne cikin matsanantan matakan tsaro a Assam a daidai lokacin da ake zaben 'yan majalisar dokoki a kasar Indiya wanda za a yi makonni biyar ana yi.

An dade ana fama da kiyayya da zargin satar filaye a Assam tsakanin 'yan kabilar Bodo da kuma dubban 'yan kabilar Bengali Musulmi, wadanda da yawan su zuwa suka yi daga yankin gabashin Pakistan kafin ya zama Bangladesh a shekarar Alif dari tara da saba'in da Daya (1971).

A shekarar 2012 ma fadan kabilancin da aka yi a wannan yanki na jahar Assam, yayi sanadiyar mutuwar mutane 100 a kalla, kuma ya tarwatsa wasu mutanen fiye da dubu 400.

A arewa maso gabashin kasar Indiya kungiyar National Democratic Front of Bodoland na daya daga cikin dimbin kungiyoyin 'yan tawayen da ke yakin neman warewa suka kafa kasar su, su kadai.