Jami'ai a Kamaru sun ce mutane na sake tserewa daga garuruwan da ke yammacin kasar, yayin da ‘yan aware ke kafa shingayen tare ababen hawa a kan tituna, suna kona ababen hawan da kuma yin awon gaba da fararen hula tare da azabtar da su domin neman kudin fansa.
Kungiyoyin rajin kare hakkin bil adama na zargin gwamnatin kasar ta Kamaru da yin sakaci da yin watsi da fararen hula da ake zalunta.
Wani mayaki da ke barazana da wukake da bindigar AK-47 ya ce zai yanke wuyar duk wani farar hula da ya ki bada hadin kai ga 'yan aware a Ngoketunjia, Bui da Mezam, wuraren gudanarwa a yankin Arewa maso Yammacin Kamaru.
Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun ce fadan da ake gwabzawa a halin yanzu, tare da ta’asar da sojojin gwamnati da ‘yan aware suka aikata, ya raba fararen hula da dama da gidajensu ciki har da ‘yan gudun hijira na baya-bayan nan da suka koma gida.
Gaby Ambo, babban daraktan kungiyar FGI mai hedikwata a Bamenda babban birnin yankin Arewa maso Yamma, ya ce fararen hula sun fusata musamman saboda gwamnatin Kamaru ba ta yin abin da ya dace na kare mutane da dukiyoyinsu.