Abin mamaki, 'yan shekaru bayan da sauran kasashen Afirka su ka taimaka ma Afirka Ta Kudu a gwagwarmayar neman 'yanci, sai kuma gashi 'yan kasar na dada tsanar 'yan sauran kasashen Afirka da sauran baki da ke kasar.
WASHINGTON D.C. —
Hare-hare masu nasaba da tsanar ‘yan kasashen waje sun karu a Afirka Ta Kudu cikin makonnin da su ka gabata, ta yadda aka kashe ‘yan kasashen waje akalla hudu a wasu tashe-tashen hankula da mafusatan ‘yan kasar su ka yi, saboda zargin wai ‘yan kasashen wajen na raba su da ayyukan yi.
Da safiyar jiya Jumma’a ma, wata sabuwar jam’iyyar siyasa mai tsanar ‘yan kasashen waje ta yi gangami a birnin Johannesburg, inda ta bukaci duk wanda ba dan kasar ta Afirka Ta Kudu ba ne ya fice daga kasar.
Masu zanga-zangar, wadanda su ka yi maci a tsakiyar birnin Johannesburg, sun bukaci da a tasa keyar duk wani bakon haure daga kasar zuwa karshen wannan shekarar.