'Yan Adawar Nijar Sun Kulla Sabon Kawance

Shugaban sabon kawance ke saka hannu a yarjejeniyar da suka yi

Biyo bayan wargajewar kawancen siyasar da suka kulla domin kalubalantar jam'iyyar dake mulki a zaben shugaban kasa, ya zama wajibi jam'iyyun da suke son cigaba da adawa su hada kansu.

Kimanin jam'iyyun siyasa goma ne a karkashin jagorancin jam'iyyar MODEL Lumana Afirka ta tsohon kakakin majalisa Hamma Ahmadu da MNRD Hakuri ta tsohon shugaban kasa Muhamman Usman suka kulla sabon kawance na FRDDR dake nufin bude sabon babin siyasa.

Wannan sabon yunkurin ya zama wajibi ne bayan da babbar kawarsu MNSD Nasara ta sanar da ficewa daga tsohon kawancen da zummar shiga gwamnatin Muhammad Issoufou na jam'iyyar PNDS mai mulki.

Sabon kawance ya kuduri aniyyar yakar wasu miyagun dabi'un da suka ce sun zama ruwan dare gama gari.

Kakakin FRDDR yace kasar na fama da cin hanci da rashawa, rashin 'yanci, musamman ga 'yan jarida, kamawa datsare 'yan adawa ba gaira ba dalili da dai sauransu.

To saidai kakakin jam'iyyar PNDS mai mulki Alhaji Asumana Muhammadou yace su 'yan adawa ya kamata su yi kuka domin su suka rasa babbar kawa. Yace idan babu 'yanci ba zasu iya kulla kawance ba. Dangane da almundahana yace su kawo shaida kowa ya gani.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Adawar Nijar Sun Kulla Sabon Kawance - 2' 48"