'Yan Adawa Sun Yi Watsi da Shirin Kara Yawan 'Yan Majalisar Jamhuriyar Niger

Shugaban kasar Niger Mahamadou Issoufou

A taron manema labarai da gungun jamiyyun adawa na kasar Niger suka kira sun nuna rashin jin dadinsu akan aiki da dokar karin yawan 'yan majalisu

A nasu ra'ayin dokar bata cancanta ba domin bata bi ta majalisar tuntubar juna ba ta alamuran siyasa.

'Yan adawan sun ce yin hakan da gwamnati tayi na nuna alamomin wasu salon yin murdiya da aiwatar da magudi da gwamnatin ke shirin yi a zaben majalisun dokoki mai zuwa a shekarar 2016.

Alhaji Dudu Rahama kakakin kawancen 'yan adawa na IRDR ya rantse ba zasu yadda da duk wani zaben dake da suddabaru ba. Yace suna ganin irin abubuwan dake faruwa shi yasa suna nemar ma kasar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kwanciyar hankalin dam Niger shi ne arzikinsa. Ba'a taba yin wani abu ba na zabe da ya kawo rigima a kasar. To amma suna ganin wannan gwamnatin zata shuka iri da zai haifar da rikici wanda kasar zata shiga.

Abun da ya kamata a tattauna a zauren taron tuntubar juna akan alamuran siyasa sai gashi an daukeshi an kaishi zauren majalisa.

Daga bangaren gungun jam'iyyun dake mulki sakataren yada labarunta Alhaji Asmanu Muhammed yace abun da gwamnati tayi kaida ce da batun kyautata kundun tsarin mulkin kasar da mahukuntan suke son suyi ya haifar da cecekuce. Yace suna aiki da doka ne ba zancen siyasa ba. Idan sun yi aiki da doka to an kawar da batun siyasa. Yace su 'yan adawa sun yi tawaye a majalisar tuntubar juna. Su 'yan adawa su ne suka ki yadda da majalisar ta tuntubar juna. Sai da suka yi tawaye na wata guda kafin su koma.

Takaddamar ta barke ne yayain da gwamnati ta mikawa majalisar dokokin kasar bukatar fadada majalisun dokokin kasar. Nan ne 'yan majalisar zasu yi nazari tare da saka mata hannu ta kasance doka.

Kawo yanzu kidigdiga sun nuna cewa kasar nada mutane miliyan 17 kuma ya kamata a ce kowadanne mutane 100,000 suna da wakili daya a majalisar dokoki.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Adawa Sun Yi Watsi da Shirin Kara Yawan 'Yan Majalisar Jamhuriyar Niger - 3' 28"