'Yan Adawa Sun Kauracewa Taron Jin Shawarwari Akan Kundin Zaben Nijer

Yau Alhamis kwamitin da aka dorawa alhakin nazari don zakulo shawarwarin gyaran fuskar kundin zaben jamhuriyar Nijer ya gabatar da rahotonsa a gaban taron majalisar CNDP da ya gudana a karkashin jagorancin firai ministan Nijer Brigi Rafini, sai dai ‘yan adawa ba su halarci taron ba.

Ayoyin doka sama da 30 na kundin zaben kasar ta nijer ne kwamitin ya yi nazari akansu a tsawon makwanni 4 na wannan aiki dake hangen kawo karshen korafe korafen ‘yan adawa wadanda ke zargin bangaren rinjaye da cusa wasu miyagun matakai a can baya da nufin tafka magudi a zabukan da za a yi a shekarar 2020 da 2021. Sakataren kula da harkokin zabe a jam’iyyar PNDS mai mulki Boubakar Sabo, mamba ne a kwamitin kwaskware kundin zabe yace, don kasa ake yin zabe ba don wani ba kuma fatansu shine a yi zabe lami lafiya

Sai dai mambobin kwamitin sun kasa cimma matsaya akan wasu muhimman ayoyin doka, dalili kenan da bangarorin suka fara neman hanyoyin warware wannan kulli inji Hambali Dodo na kawancen jam’iyyu ‘yan ba ruwanmu.

Jam’iyyun adawa na gamayyar FRDDR wadanda tun da farko suka fice daga kwamitin nazarin hanyoyin kwaskware kundin zabe sun kauracewa taron gabatar da rahoton shawarwarin da aka zo da su, a cewar wani kakakinsu Maman Sani Adamou.

To amma masu mulki na ganin rashin halartar ‘yan adawa a wannan aiki ba zai katse masu hamzari ba.

Bayan majalisar CNDP mai alhakin warware rigingimun siyasa ta nazarci sauye sauyen da kwamitin ya aiwatar, gwamnati za ta gabatar da wadannan kudirorin a gaban majalisar dokokin kasa domin ta tabbatar da su a matsayin dokokin zabe.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Adawa Sun Kauracewa Taron Jin Shawarwari Akan Kundin Zaben Nijer - 2'58"