YAMAL: MDD Ta Kira Bangarorin Dake Fafatawa Su Fice Daga Tashar Jiragen Ruwan Hodeida

Tashar Jiragen Ruwam Hodeida

Majalisar Dinkin Duniya na bukatar tashar jiragen ruwan Hodeida dake kasar Yamal domin kai dokin gaggawa wa mutane kimanin dubu dari shida dalili ke nan da kwamitin sulhun majalisar ya umurci duk fasu fafatawa da juna su fice daga tashar

Jiya Alhamis Kwmitin Sulhun MDD ya yi kira ga dukkannin bangarorin dake fada a kasar Yamal da su bar tashar jiragen ruwa ta Hodeida a bude, a yayin da masu ayyukan jinkai ke kokarin kai kayakin agaji ga farar hula kimanin 600,000 a cikin birnin.

Mambobin Kwamitin sun yi taron gaggawa a sakaye, bayan da gamayyar da Saudiyya ke jagoranta ta shiga kai hare-haren jiragen sama kan Hodeida da safiyar shekaran jiya Laraba, bayan abin da daya daga cikin mambobin gamayyar,wato Hadaddiyar Daular Larabawa, ta kira cikar wa'adin lokacin da ya kamata 'yan Houthi masu samun goyon bayan kasar Iran su mika tashar jirgin ruwan, wadda ke da matukar muhimmanci a gabar tekun bahar al-Ahmar.

"Lokaci ya yi da ya kamata Kwamitin Sulhun ya kira da a gaggauta kawo karshen hare-haren soji kan Hodeida," a cewar Jakadan kasar Swedin a MDD Carl Skau a gabanin taron.

Ya kara da cewa, "Ana bukatar hakan saboda Manzon Musamman na MDD da kuma sauran masu taimakawa su samu sukunin kawar da bala'i da kuma samar da mafita mai dorewa a siyasance."