Yakin Neman Zaben Shugaba Buhari a Taraba Ya Bar Baya Da Kura

Biyo bayan asarar rayuka da Kuma lalata allunan kanfen da aka yi a yayin ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari ya kai jihar Taraba, yanzu haka wata sabuwa ta kunno kai a tsakanin gwamnatin jihar da kuma bangaren APC.

Ziyarar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai jihar Taraba ta bar baya da kura, domin kuwa baya ga asarar rayuka sakamakon turmitsittsin da aka yi, an kuma farma wasu akan hanya abinda ‘yan jam’iyyar APC ke zargin gwamnatin jihar da daukar nauyin harin da kuma lalata allunan kamfe, sai dai gwamnatin PDP a jihar ta musanta wannan zargin.

Ambassada Hassan Jika Ardo, na cikin dattawan jam’iyyar APC a jihar, yace suna da shaidun dake tabbatar da hannun gwamnatin jihar a wannan lamarin.

To sai dai kuma a martanin da ya maida gwamnan jihar a ta bakin hadimin sa a bangaren harkokin siyasa, Abubakar Bawa, yace shafa musu kashin kaji ake yi.

Jama'a da dama ne aka raunata sanadiyar harin na ‘yan bangar siyasa. Mallam Isa Jalo, wani dan jarida ne, shi ma yana cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya a hannun wasu ‘yan bangar siyasa.

Ga karin bayani cikin sauti daga Ibrahim Abdul'aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Yakin Neman Zaben Shugaba Buhari a Taraba Ya Bar Baya Da Kura - 3'30"