Jam'iyyu 55 da kuma 'yan takarar shugabancin kasa 22 na babban zaben kasar Zimbabwe da ke tafe, na ta alkawura iri guda amma ta wajen amfani da kalamai iri daban-daban na tallata manufofin nasu; da su ka hada da alkawarin sauye-sauye, da samar da ayyukan yi da tattalin arziki mai inganci.
Wannan dai kusan wani sabon salo ne a kasar da ta shafe shekaru kusan 40 karkashin mulkin mutum guda, Robert Mugabe.
Ranar Litini kasar za ta gudanar da zabe mai kafa tarihi, a karo na farko cikin shekaru 38 ba taru da Mugabe ya shiga sahun 'yan takara ba. To amma masu kada kuri'a da masu saka ido duk na taka tsantsan wajen bayyana kwarin gwiwarsu, saboda fargabar da ake da ita kan ko shin za a yi zaben cikin adalci da sahihanci - da kuma shin ko wanda ya yi nasara zai ciki alkawarin kawo canje-canjen.
A wannan kasa mai dauke da mutane miliyan 5 da su ka cancanci kada kuri'a, ba kowa ne ya yi imanin cewa za a ga wani canji ba.