Yakin neman magunguna masu saukin kudi ya koma daga HIV zuwa Hepatitis

Kwayoyin magunguna

Wani sabon yaki na neman samar da magunguna masu saukin kudi a kasashe masu tasowa yana nan yana shirin - a wannan lokacin, domin warkar da cutar hepatitis C - fiye da shekaru goma bayan yaki kan kudaden maganin kanjamau a Afirika.
Wani sabon yaki na neman samar da magunguna masu saukin kudi a kasashe masu tasowa yana nan yana shirin - a wannan lokacin, domin warkar da cutar hepatitis C - fiye da shekaru goma bayan yaki kan kudaden maganin kanjamau a Afirika.

Magugunan zamani da aka kaddamar a kasuwannin yamma zasu iya warkar da cutar hanta ko kuma kawar da cutar baki daya daga miliyoyin mutane kama daga kasar China zuwa Kongo. Amma wannann ba zai yiwu ba sai idan kudaden maganin sun sauko sosai.

Kamfanin hada magunguna kamar su Gilead Sciences, wandanda ke yin kwayar maganin da ake kira Sovaldi wani magani da aka amince da shi a Amurka wanda kuma kudin maganin yini guda yakan kai har dolla 1,000, suna shan matsi da su rage kudaden magungunan su domin kaucewa irin arangamar da ta faru a farkon fitowar maganin kanjamau.

“Samar da maganin wani muhimmin abu ne na gaggawa kuwa,” Darakatan janar na WHO Margaret Chan ta gayawa Reutas a zuwanta ziyara a London.

“Wadannan magunguna suna da tsada kwarai. Ta yaya zamu iya fuskantar wannan? Ina fata zamu koya daga darasin kanjamau mu kuma iya warware wannan matsalar ba tare da an yi fito na fito ba.”

A shekaru na 1990, magungunan kanjamau da ake sayef a fiya da dola 10,000 kan kowanne mara lafiya a shekara, sun fi karfin miliyoyin mutane a kasashe masu tasowa na duniya. A yau, godiya ga magunguna masu saukin kudi da ake samu daga Indiya kudin maganin ya sauka zuwa dola 100 ga matalauta na duniya.
Kamar su kanjamau, za’a iya yada hepatitis C (HCV) ta jini, sau da yawa kuma ana samu ta wurin allurai marasa kyau. Bisaga kiyascin kugiyar lafiya ta duniya mutane miliyan 150 a dukan duniya sun kamu sosai da Hepatitis C wanda zai iya sa su hatsarin kamuwa da ciwon hanta.

Sai dai kuma yayin nawayar HIV yafi yawa a Afrikan ta kudu da Sahara, yawancin masu dauke da Hepatitis C suna kasashe masu matsakancin taltalin arziki kamar su China da India da Rushiya, inda kamfanin magunguna ke nokewa amincewa da farashi mai sauki.