Wata babbar tawagar gwamnatin Janhuriyar Nijar, karkashin Ministan Tsaron kasar, Dakta Alkash Alhada ta jagoranci wani muhimmin taro na masu ruwa da tsaki kan batun tsaro a jahar Tahoua (Tawa) mai makwabtaka da kasar Mali, wadda ke fama da ‘yan ta’adda da kan ketara kan iyaka zuwa kasar Nijar su aikata ta’asa.
Taron, wanda aka yi shi da shugabannin jama’a da kuma na bangaren tsaro da ‘yan majalisun dokoki na kasa da Gwamnan jahar Tahoua da sarakunan gargajiya da shugabanin addinai da kungiyoyin farar hulla da na mata da na matasa da na ‘yan siyasa domin ankarar da al'ummar jahar Tahoua game da barazanar tsaro dake wannan jaha mai makwabtaka da azabtacciyar kasar ta Mali ke fuskanta.
Minista Alhada ya ce ganin muhimmancin bayar da hadin kan al’ummomin yankin Tahoua ya sa tawagar ta gwamnatin Nijar ta yanke shawarar kaddamar da kwamitocin da za su karade fadin jahar ta Tahoua su nemi hadin kan jama’a wajen yaki da ‘yan ta’adda. Ya ce yaki da ‘yan ta’addan wani babban jihadi ne. Wani malami a tawagar ya jaddada cewa akidar ‘yan ta’addar sam ba ta yi kama da ta Musulunci ba.
Ga Haruna Mamman Bako da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5