A karshen mako, wata kungiyar mai yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi, ta shirya taron lakca a Kano, game da rawar kafofin yada labarai ke takawa wajen dakile annobar shaye-shaye, a tsakanin matasa da kuma bangar siyasa.
Sai dai masana harkokin sadarwa na ganin cewar, yakin ba na kafofin yada labarai ne ba su kadai ba.
Comrade Mukhtari Iliyasu, shine shugaban kungiyar 'Initiative for fighting against Drug Abuse and Enlightment' wadanda ke wayar da kan jama'a kan illar miyagun kwayoyi.
Dr. Sanusi Iguda malami a tsangayar nazarin aikin jarida da sadarwa ta jami'ar Bayero Kano shine ya gabatar da makala a wurin taron.
Baya ga shuwagabannin kafofin yada labarai da masana a fannin aikin jarida, dalibai daga makarantun ilimi mai zurfi daban daban ne suka halarci taron.
Sai dai 'yan siyasa sun kauracewa zauren taron, wanda aka shirya akan Hajiya Hafsa Umar Ganduje mai dakin gwamnajihat Kano zata kasance babbar bakuwa, duk da cewa alkibilar taron dai wanda ya wakana a cibiyar nazari, da bada horo kan harkokin demokradiyya ta Mumbayya a jihar Kano.
Itace ta ankarar da masu ruwa da tsaki musamman 'yan siyasa game da illar bangar siyasa, da akan tsoma matasa cikin ta hanyar amfani da miyagun kwayoyi.
Ga rahoton wakilin shashen Hausa na Muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5