Gwamnatin jihar Bauchi ta kulla yarjejeniya da hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi da fataucinsu, NDLEA, domin magance matsalar tu’ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin matasa da ke sa su kaddamar da ayyukan ta’addanci irinsu Sara Suka da kuma 'Yan Bakin Boda.'
Gwamnan jihar, Senata Bala Abdulkadir Muhammad, ya cimma yarjejeniyar ce a lokacin da sabon kwamnandan NDLEA din ya ziyarci gwamnan a gidan gwamnatin jihar a Bauchi.
Da ya ke marabtan Kwamandan hukumar yaki dashan miyagun kwayoyi, Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad, ya yabawa hukumar dangane da gagarumin aikin dasukeyi na dakile matsalar tu’ammala da miyagun kwayoyi dake illatar da matasa, inda ya bukaci ganin yakin bawai kawai ya tsaya kan matasaba,a fadadashi har zuwa kan masu safara dakuma saida kwayoyin.
Tunda farko, Kwamanadan hukumar NDLEA na shiyyar Bauchi, Malam Ali Aminu, ya jaddada wa gwamnan samun dukkan goyon bayan hukumar don tabbatar da an tsarkake jihar Bauchi daga wannan musiba na amfani da miyagun kwayoyi.
Ya ci gaba da cewa a matsayinsa na kwamandan hukumar a Bauchi, "ina shaida maka yawan tu’ammali da muggan kwayoyi a jihar ya ta’azzara, wannan yanayi ya na nuna cewa matsalar a jihar ta na da ban tsoro. Hakan na bukatar kowa da kowa ya bada gudumowa don kare abun kaunarmu."
Wani mahaifi, ya yi na’am da wanan yunkuri da gwamana Bala Abdulkadir Muhammad (Kauran Bauchi) ya dauka na hada hannu da hukumar NDLEA don yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi:
Saurari rahoton Muhammad Abdulwahab:
Your browser doesn’t support HTML5