Ministan Harkokin Wajen Kamaru, Lejeune Mblella Mbella, ya gana da tawagar Kungiyar Tarayyar Turai a ofishinsa da ke Yaounde, babban birnin kasar game da matsalolin da su ka hada da na tsaro, musamman ma aika-aikar Boko Haram. Wakiliyar EU ta musamman Francois Colle ta mika gudunmowar CFA din Kamaru miliyan 32 ga Mr. Mbella a matsayin gudunmowar kungiyar ta EU a yakin da kasar ke yi da ‘yan ta’adda irin Boko Haram.
Da ta ke jawabi, Francois Colle ta ce kungiyar ta EU ta kuduri aniyar yaki da Boko Haram babu kakkautawa ta wajen taimakawa ma ‘yan Boko Haram. Da Ministan ke karbar gudunmowar, ya yaba da irin gudunmowar da kingiyar ta EU ke bayarwa wajen yaki da Boko Haram.
Shi ma Ministan Lafiya na kasar Andre Mama Fouda ya bayyana yadda ake gudanar da allurar rigakafi a kasar Kamaru, inda ya ce kasashen duniya da kungiyoyi irin na Rotary sun yi ta taimakawa kuma su na kan taimakawa wajen ayyukan rigakafin tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Lafiyar kasar ta Kamaru. Ya ce kusan kowani aikin yekuwa na cin akalla CFA miliyan guda. Ministan ya ce aikin na riga kafi ya taimaka wajen rage yawan kamuwa da cututtuka da yara ke yi a kasar.
Your browser doesn’t support HTML5