Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya Manjo-Janar Tukur Yusuf Brutai ya ce wutar da ‘yan Boko Haram ke sha ce ta sa su shiga kai hare-haren kunar bakin wake don su nuna har yanzu sun a nan, alhalin kuwa tasu ta kusa karewa.
Don haka wakiliyarmu a shiyyar Filato Zainab Babaji ta tuntubi wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum mai suna Dan Manjang don jin yadda yak e ganin al’amuran tsaro a Najeriya a yanzu sai ya yi nuni da kudurin Janar Burutai na cimma wa’adin da Shugaba kasa a ba sojojin Najeriya. To amma y ace kodayake akwai fatan a gama da Boko Haram cikin wa’adin na Shugaban kasa, da wuya a iya cimma wannan wa’adin. Y ace ai ba a Naijeriya kawai Boko Haram su ke ba.
Game da cigaba da kai hare-haren da ‘yan Boko Haram ke yi, Manjang y ace ya kamata mutane su gane cewa yaki da ta’addanci ba aikin gwamnati ba ne kawai, na kowa da kowa ne. Y ace ba jami’an gwamnati ‘yan ta’addar ke kashewa ba, jama’a ne; kuma gashi babu yadda ‘yan ta’addar za su shiga cikin jama’a ba tare da sanin kowa ba. Ya ce da gwamnati da jama’a - kowa da rawar da ya kamata taka.
Ga Zainab da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5