Yayin da Gwamnatin Buhari ke harmar bayyana sunayen wadanda su ka sace kudaden Najeriya su ka boye a Dubai, har a bin ke kawo cece-kuce, ‘yan jam’iyyarsa ta APC sun ce a shirye su ke su kare manufofin Shugaba Muhammadu Buhari na yaki da al’mundahana saboda barnar da aka yi ta na da yawan gaske.
Sakataren jam’iyyar APC Mai Mala Boni ya ce wannan badakalar ta wuce batu siyasa - ta na da girman gaske. Ya kara da cewa duk cikin wadanda aka ce sun ci kudin babu wanda y ace bai ci ba; saidai kawai y ace bas hi kadai ya ci ba.
‘Yan babbar jam’iyyar adawa ta PDP na zargi da kuma bayyana damuwar cewa yaki da almundahanar da APC ke yi na iya zama, koma ta ma zamo wata hanyar yin bita da kulli ga ‘yan PDP saboda gabar siyasa, inda su ke nuni da tsare babban Sakatarensu Olisa Metuh da sauran gagga-gaggansu.
Saidai wasu ‘yan PDP din na cewa duk da hidima da dawainiyar da su ka rinka yi ma jam’iyyar, ba a yi rabon kudin sayo makamai da ake zargin an yi da su ba. Jagoran addu’a a dandalin yakin neman zabe na PDP, Lamido Cikere, y ace sam ba a yi rabon kudin sayo makaman da aka hamdame da shi ba.
Ga wakilinmu Nasiru Adamu el-Hikaya da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5