Jami’an kiwon lafiya a Najeriya, na kokarin fadakar da kan al’umma akan barkewar cutar Ebola, wadda tayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 900 a kasashen yammacin Afrika.
An sami labarin cewa mutane 7 ne suka kamu da cutar a Najeriya. Biyu daga cikin su sun mutu, wanda ya fara mutuwar dai dan kasar Laberiya ne wanda asali shi ne ya shigo da cutar Najeriya da kuma wata ma’aikaciyar asibiti wadda ta yi jinyar sa a wani asibiti da ke birnin Ikko. Sauran mutane biyar din kuma an killacesu a wuri na musamman don kula da su.
A hirar da ma’aikacin muryar Amurka Aliyu Mustapha yayi da karamin Ministan kiwon lafiya, Dr. Halliru Al-Hassan, ya fadi cewa an shinfida matakai akan ganin marasa lafiyar, musamman malaman asibiti. Matakan sun hada da sanya safar hanu, rufe hanci da baki da kuma yin kafa-kaffa da duk wani abu dake fitowa daga jikin mara lafiyar, kamar jini, fitsari, majina da sauransu.
Ministan ya kara da cewa, Bincike ya nuna cewa mutane 70 ne suka yi chudanya da bakon da ya shigo da cutar. Kuma an dauki matakan bincike don tabbatar da cewa basu kamu da cutar ba. Hakan ya sa aka iya gano mutane 6 da suka kamu da cutar a Najeriya.
Bugu da kari, an dauki matakan bincike na tantance pasinjoji masu shigowa Najeriya daga wata kasa, ta jirgin sama, ko jirgin ruwa don iya tantance ko suna da cutar.
Your browser doesn’t support HTML5