Yajin Aikin ‘Yan A Daidaita Sahu Ya Shiga Rana Ta Biyu A Kano

Baburan A Daidaita Sahu a Kano (AP)

Gabanin hakan dai, gwamnati ta nanata cewa, batun biyan wadannan kudade yana nan daram, amma  ta roki ‘yan sahun da su hakura da yajin aikin nasu.

Yayin da aka shiga rana ta biyu da fara yajin aikin da masu tuka baburan A Daidaita Sahu suka fara Kano, wanda ya gurgunta harkokin sufuri a birnin da kewayen Kano, masu kula da lamura na ci gaba da bayyana hanyoyin magance yawaitar takaddamar dake wakana tsakanin gwamnati na direbobin na A daidaita sahu.

Batun sabunta rijista akan kudi kimanin naira dubu 10 baya ga kudaden da gwamnatin Kano ke karba a kullum a hannunsu, na cikin dalilan yajin da ‘yan sahun suka daka.

Abdulkarim Yusuf babban sakataren gamayyar kungiyoyin direbobin Babura masu kafa uku a jihar Kano ya ce a wancan lokaci mambobinsu sun yi rijista a baya.

Gabanin haka dai, gwamnati ta nanata cewa, batun biyan wadannan kudade yana nan daram, amma ta roki ‘yan sahun da su hakura da yajin nasu.

Baffa Babba Dan Agundi shi ne shugaban hukumar KAROTA mai kula da zirga zirgar ababen hawa ta Kano ya ce sun yi rarrashi ‘yan A daidaita Sahun da kada su shiga yajin aikin.

Kimanin kashi 90 na zirga-zirgar mutane a birnin Kano ta gurgunce sanadiyyar wannan yajin aiki.

Tun a shekara ta 2004 ne gwamnatin ta Sanata Ibrahim Shekarau ta bullo da tsarin sufurin Adaita Sahu.

Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa daya ne daga cikin wadanda suka shawarci gwamnatin ta kafa wannan tsari a wani mataki na kawo karshen amfani da baburan achaba a wancan lokaci.

Baya ga kaucewa manufar farko ta samar da sufurin a daidaita sahu a Kano, gazawar gwamnatin wajen samar da sauran kafofin sufuri na kara zafin takaddama tsakanin ta da ‘yan sahun, Inji Malam Kabiru Saidu Sufi.

A cikin watan Satumbar bara ne, majalisar dokokin Kano ta amincewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ciyo bashin kimanin naira miliyan 500, dayace zai sayo motocin safa na sufurin mutane a birnin da keayen Kano.

Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

Yajin Aikin ‘Yan A Daidaita Sahu Ya Shiga Rana Ta Biyu A Kano - 3'30"