Yajin Aikin 'Yan A Daidaita Sahu Ya Farfado Da Sana'ar Acaba A Kano

'Yan Acaba a Najeriya

Shekaru goma da suka wuce hukumomin Kano suka haramta sana'ar Acaba saboda hadurran da suke janyo wa.

Rahotanni daga Kano a Najeriya na nuna cewa, sana’ar Achaba ta dawo a birnin, kimanin shekaru goma da haramta ta. Hakan ya biyo bayan yajin aikin da direbobin Babura masu kafa uku wato Adai-daita sahu keyi ne wadda ya shiga rana ta uku a yau laraba.

Rahotanni daga Kano a Najeriya na nuna cewa, sana’ar Achaba ta dawo a birnin, kimanin shekaru goma da haramta ta. Hakan ya biyo bayan yajin aikin da direbobin Babura masu kafa uku wato Adai-daita sahu keyi ne wadda ya shiga rana ta uku a yau laraba.

Sai dai hukumomin jihar ta Kano sun umarci kamfanin sufuri mallakar gwamnatin jihar wato Kano line, ya jingine jigilar fasinjoji dayake yi a tsakanin jihohin kasar, ya mayar da zirga zirgar sa zuwa cikin birnin da kewayen Kano, domin saukakawa mutane wahalhalun sufurin da suke fuskanta sanadiyyar wannan yajin aiki na direbobin Baburan adai-daita sahu.

Alhaji Muhammad Mahmud Santsi, kwamishinan sufuri da gidaje na jihar Kano ya ce baya ga haka gwamnati na daukar matakan samar da motocin safa safa guda 100 da zasu rinka zirga zirga da nufin inganta harkokin sufuri a birin da kewayen Kano.

Yayin da gwamnati ke cewa, tana daukar matakai rage radadin wannan yajin aiki na direbobin adai-daita sahu wadda ya shiga rana ta uku, yanzu haka tsohuwar sana’ar Achaba da gwamnatin Kano ta haramta a shekara 2013 saboda dalilai na tsaro, ta yiwa birnin na Kano kome.

Dalibai da ma’aikata mata da ‘yan kasuwa na cikin rukunin mazauna Kano dake fuskantar gagarumin kalubale sakamakon wannan yajin aiki, lamarin daya sa al’uma suka fara kiraye-kirayen ayi sulhu tsakanin bangarorin nan guda.

Sai dai ya zuwa daren jiya talata, babu wani sahihin zance dake nuna zama teburin sulhun tsakanin ‘yan sahun da gwamnati, al’amarin dake nuna alamun cewa, bangarorin biyu kowa ja daga.