Najeriya-Yajin Aikin Ma'aikata Ya Shiga Yini Na Biyu.

Mataimakin shugaban Najeriya a bikin ranar ma'aikata.

Kungiyoyin kwadago za su ci gaba da yajin aikin da suka fada a jiya Alhamis, bayan zaman da suka tashi ba tareda cimma daidaito da gwamnatin tarayyar ba.

Da yake yi wa wakilin Sashen Hausa karin bayani kan zaman da suka yi da wakilan gwamnatin tarayya a Abuja, karkashin jagorancin shugabar ma'aikata uwargida Winifred Oyo Ita, kakakin kungiyar kwadago ta UTC Komored Kabir Nasir, yace gwamnati tana jan kafa cewa za su sake zama ranar 4 ga watan Oktoba, wannan ba-shine suke son ji ba.

Kakakin yace, bukatar su shine jin ranar da za'a fara aiwatar da sabon albashin ma'aikata.

Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayyar, Mrs. Winifred, tace suna aiki tukuru domin ganin an warware wannan matsala. Da kara da cewa tilas ne a yi tafiyar tareda gwamnatocin jihohi.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina

Your browser doesn’t support HTML5

An kasa cimma matsaya kan yajin aiki-2:15"