Yajin aikin da daukacin ma'aikatan jihar ke yi ya haddasa matsalar rayuwa ga al'ummar jihar soboda uay wata uku ke nan gwamnati bata biyasu albashinsu ba.
Makonni uku ke nan da ma'aikatan suka fada yajin aikin kuma kamar yadda suka fada sai illa masha allahu saboda suna bukatar gwamnati ta biyasu hakkokinsu.
Yajin aikin ya tsananta inda al'ummar jihar suka fara kokawa da lamarin.Wani Alhaji Salihu yace yajin aikin ya haddasa mutuwar mutane marasa lafiya a asibitoci.Cin abinci ya yiwa wasu wuya saboda rashin kudi. Aurarraki ma sun mutu.
Sakataren kungiyar kwadago na kasa reshen jihar Nasarawa Kwamred Ahmed Muhammad Naibi ya bayyana wasu dalilan shiga yajin aikin. Yace akwai wasu abubuwa da shekaru shida ke nan ba'a yi masu ba kaman karin girma da kuma karin albashi na shekara shekara da ba'a yi masu ba. Akwai yarjejeniya da suka yi kan biyan karamin albashi da ya kamata a biya na watanni hudu amma gwamnati bata yi ba.
Lokacin da ake tantance sunayen ma'aikata an tsallake wasu. Watanni uku ke nan wasu ma basu karbi albashi ba.
Kwamitin dake zantawa da gwamnati akan yadda za'a warware matsalar Kwamred Yusuf Iya yace har yanzu basu cimma wata matsaya da gwamnatin jihar ba saboda gwamnati ta dage sai sun janye yajin aiki kafin su zauna teburin shawara dasu. Su kuma 'yan kwadago sun ce a dokokinsu idan sun je yajin aiki sai an samu yarjejeniya kafin su janye yajin.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5