Yajin Aikin Likitoci Bai Yi Tasiri Sosai Ba a Asibitin Kasa dake Abuja

Kofar shiga asibitin kasa a Abuja

Yayinda yajin aikin da likitocin dake koyon zama kwararru a fannonin aikin likitanci dabadaban ke tasiri a wasu asibitocin dake cikin birnin Abuja a asibitin kasa harkokin asibitin na cigaba kamar yadda aka saba

Yajin aikin da likitoci suka fara yi jiya yana tasiri a wasu asibitocin dake birnin Abuja amma ban da na Gwarinpa da kuma asibitin kasa da ake kira National Hospital inda mayan likitoci ke cigaba da aiki.

Aiki a asibitin Gwarinpa na tafiya babu cikas domin duk likitocin asibitin suna aikinsu. Shugaban asibitin Dr Adebayo yace duk likitocinsa suna aiki.

Wata mai jego da aka zanta da ita ta tabbatar cewa ta samu ganin likita ba tare da wata cikas ba.

Aamma mai magana da yawun asibitin kasa Dr. Tayo Haastrup yace yajin aikin ba na gaba daya ba ne kuma bai hana manyan likitoci da ake kira Consultants ganin masu jinya ba. Sai dai likitocin dake neman kwarewa da ake kira Resident Doctors suna cigaba da yajin aiki. Basa ganin masu jinya.

Wata nas mai aiki a asibitin ta ce manyan likitoci na ganin masu jinya Ta ce babu wata matsala.

To sai dai masu son ganin likita na dakon sa'o'i fiye da yadda aka saba gani a asibitin kasa inda yanzu mutum na kai awa biyar maimakon awa daya kafin ya ga likita.

Likitocin na neman gwamnatin tarayya ta biyasu wasu albashi da alawus alawus.

Ga rahoton Sahabo Aliyu Imam da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Yajin Aikin Likitoci Ba Yi Tasiri Ba a Asibitin Kasa dake Abuja - 3' 01"