Sai dai daliban wasu daga cikin makarantu masu zaman kansu a birnin da kewayen Kano na ci gaba da daukar darasi, yayin da harabobin wasu daga cikin makarantun ke kulle.
Kazalika, ma’aikatan gwamnati sun kauracewa ofisoshin su, saboda biyayya ga umarnin kungiyar kwadagon ta kasa. Baya ga haka bankunan kasuwanci sun rufe ofisoshin su, amma wasu kamfanoni masu zaman kansu sun bude domin gudanar da ayyukan su na yau da kullum.
A hannu guda kuma, ‘yan kasuwa na ci gaba da hada-hada a kasuwanni, yayin da motocin haya da sauran ababen hawa ke gudanar da zirga zirga a titunan kwaryar birnin Kano. Kazalika, masu gidajen mai na sayar da man ga masu ababen hawa.
A jihar Jigawa kuwa, gwamnan jihar ne Malam Umar Namadi ya gabatar da kasafin kudi na badi a gaban majalisar dokokin jihar, duk kuwa da cewa, baya ga yajin aikin kungiyar kwadaon ta NLC, yajin aikin ‘yayan kungiyar ma’aikatan majalisar dokoki na jihohin Najeriya wato PASAN ya shiga mako na uku.
Kungiyar ta PASAN na daka nata yajin aikin ne a fafutikar neman gwamnoni su aiwatar da dokar tabbatar da ‘yancin kudade ga majalisar dokoki na jihohi.
Jimlar naira biliyan 298.14 ne gwamna ya kudiri aniyar kashewa a shekarar kudi ta badi wato, 2024.
Ku Duba Wannan Ma Yan Kwadago Sun Fara Siyasantar Da Ayyukan Su - ‘Yan Najeriya